Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

An Fara Wasannin Kakar Kwallon Kafa Ta 201/16 Najeriya


A jiya ne aka fara kakar wasan kwallon kafa ta shekarar 2015, da 2016 a Najeriya inda kungiyar Rivers United ta doke Eyinmba da ci 1-0 a birnin fatakwal.

Frederick Obomate ne ya sami nasarar jefa kwallon a cikin minti na 64 da fara wasan a yayin da ya buga free kick wanda ya kasance a matsayin nasarar da kungiyar ta samu akan kungiyar ‘yan wasan Elephant a cikin shekaru bakwai.

Kungiyar Newcomers kuma ta ba Nasarawa united mamaki da ci 1-0 a filin wasa na Aku Stadium a makurdi, musa Newman da Chukwuka Emmanuael kuma suka jefa kwallaye biyu kafin Ifeanyi Nweke ya rama guda.

Kano Pillers kuma ta lallasa Enugu Rangers da ci 2-1 a filin wasa na Sani Abacha dake birnin Kano, Sunshine stars kuma suka yi kunnen doki da Akwa United, kungiyar Lobi Star kuma ta doke Shooting Stars da ci 1 – 0.

Kungiyar Ikorodu United sun yi kunnen doki da Abia Warriors, Wikki Tourists kuma ta doke El-kanemi Warriors da ci 1-0 a filin wasa na karkanda stadium.

Wasan Heartland da Warriu Wolves kuma ya tashi babu ci ko guda, yayin da FC IfeanyiUbah kuma ta doke Giwa FC da ci 1-0

  • 16x9 Image

    Ibrahim Jarmai

    Ibrahim Jarmai, ma’aikacin jarida (International Broadcaster Multi Media) a sashen Hausa na muryar Amurka, mai gabatar da shirye shirye a radio da talabijin, da kuma shafukan yanar gizo, dan asalin jihar Kasina.

XS
SM
MD
LG