Yadda Sakamakon Gasar Cin Kofin Zakaru Ya Kasance

Kungiyar kwallon kafa ta Barcelona ta doke Inter Milan na kasar Itali daci 2-0 a gasar cin kofin zakarun Nahiyar turai na 2018, zuwa 2019 a matakin wasan rukuni zagaye na uku.

A sauran wasannin da aka buga aranar laraban da ta gabata PSV sunyi 2-2 da Tottenham, sai kuma Club Brugge da Monaco 1-1 Borussia Dortmund ta lallasa Athletico Madrid da kwallaye 4-0.

Itama Kungiyar Liverpool na kasar Ingila ta doke Crvena da ci 4-0, Lokomotiv Moscow tasha kashi a gidanta daci 3-1 a hannun FC Porto, PSG da Napoli 2-2, Galatasaray 0- 0 Schalke 04, Bayan kammala wasan zagaye na uku a gasar ta cin kofin zakarun Nahiyar turai a matakin rukuni ga yadda jaddawalin teburin yake na rukuni rukuni.

Ku Duba Wannan Ma Babu Alamun Dan-Wasa Anthony Martial Zai Bar Kungiyarsa

Rukunin (A) 1) Borussia Dortmund Maki 9, 2) Athletico Madrid Maki 6, 3) Club Brugge Maki 1, 4) Monaco Maki 1, Rukunin (B) 1) Barcelona Maki 9, 2) Inter Milan Maki 6, 3) Tottenham Maki 1, 4) PSV Maki 1, Rukunin (C) 1) Liverpool Maki 6, 2) Napoli Maki 5, 3) Paris-saint Germany Maki 4, 4) Crvena Maki 1.

Rukunin (D) 1) FC Porto Maki 7, 2) Schalke 04 Maki 5, 3) Galatasaray Maki 4, 4) Lokomotiv Moscow Maki 0, A rukunin (E) kuwa Kungiyar kwallon kafa ta Ajax tana jan ragamar da maki 7, Bayern Munich tana mataki na biyu da maki 7, Benfica da maki 3 sai AEK Ethens 0.

Rukunin (F) 1) Manchester City Maki 6, 2) Olympicos Lyon Maki 5, 3) Hoffenhiem Maki 2, 4) Shakhtar Donest Maki 2, Rukunin (G) 1) Roma Maki 6 2) Real Madrid Maki 6, 3) CSKA Moscow Maki 4, 4) Viktoria plzen Maki 1.

Rukunin (H) 1) Juventus Maki 9, 2) Manchester United Maki 4, 3) Valencia
Maki 2, 4) Young Boys Maki 1.

Your browser doesn’t support HTML5

Yadda Sakamakon Gasar Cin Kofin Zakaru Ya Kasance 3'20"