Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Ana Rade-Radin Kocin Real Madrid Julen Zai "Kara Gaba"


Akwai hasashen kocin Kungiyar kwallon kafa na Real Madrid bangaren matasa Team B, Santiago Solari, ya maye gurbin babban Kocin Kungiyar ta Real Madrid Julen Lopetegui, na wucin gadi wanda ake hasashen cire shi, sakamakon yanayin da Kungiyar ta shiga na rashin samun nasara a wasanni uku a jere.

Rabon da kungiyar ta samu kanta a irin wannan yanayi tun shekara ta 2006/07.

A ranar Asabar da ta gabata Real Madrid ta sha kashi a Bernabeu a hannun Kulob din Levante da ci 2-1 a gasar La liga da ta buga a bana.

Wanda sakamakon ya kara jefa kocin Julen Lopetegui, cikin matsatsi, lamarin da ya sa kungiyar ta Real ta dawo matsayi na biyar a teburin gasar La liga a mako na tara.

Sai dai tun kafin wasan na ranar Asabar da Real Madrid ta yi, daraktan kungiyar Emilio Butragueno, ya nuna goyan bayansa ga kocin Lopetegui.

Sai dai yanzu za su fuskanci matsin lamba ganin yadda za su fafata a wasu manyan wasanni, da suka hada da gasar zakarun Nahiyar turai, da kuma babban wasan hamayya wato El-Clasisco tsakanin su da kungiyar Barcelona, a karshen mako na gaba.

please wait

No media source currently available

0:00 0:01:43 0:00
  • 16x9 Image

    Yusuf Harande

    Yusuf Aliyu Harande, dan jaridar sashen Hausa na gidan radiyon Muryar Amurka (VOA). Dan asalin Hiliya a karamar hukumar Tambuwal, jihar Sakkwato.

Facebook Forum

XS
SM
MD
LG