Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Mourinho Na Fuskantar Bincike Kan Yin Sakaci


Rahotanni na nuni da cewar kociyan Kungiyar kwallon kafa ta Manchester United Jose Mourinho, yana fuskantar bincike daga Jami'an gudanarwa na Kungiyar ta United, kan zarginsa da ake yi na yin sakaci.

Ana zargin shi ne da bari jerin sunayen 'yan wasansa 18 da suka fafata da Kungiyar Chelsea suka bayyana kafin ranar wasan da suka taka a gasar Firimiya ta Ingila.

An tashi a wasan da ci 2-2 wanda aka buga a gidan Chelsea.

A gefe guda kuma, bayanai na nuni da cewar Mourinho, na fuskantar barazana daga hukumar kula da wasan kwallon kafa ta Ingila (FA) na dakatar da shi a kan layi yayin da Manchester za ta yi wasa sakamakon hayaniya da sukayi, da mataimakin kocin Chelsea Marco Ianni a filin wasa na Stamford Bridge.

Lamarin ya faru ne a ranar Asabar a gasar mako na goma na Firimiya lig a bana bayan da Chelsea ta farke kwallonta a mintuna na 96 daf da tashi inda aka tashi 2-2.

Shi kuwa danwasan gaba na kasar Faransa da Manchester United Anthony Martial, mai shekaru 22, da haihuwa ya musanta rade radin da ake ta yi cewa yana da matsala tsakaninsa da kocinsa Mourinho.

please wait

No media source currently available

0:00 0:01:52 0:00

  • 16x9 Image

    Yusuf Harande

    Yusuf Aliyu Harande, dan jaridar sashen Hausa na gidan radiyon Muryar Amurka (VOA). Dan asalin Hiliya a karamar hukumar Tambuwal, jihar Sakkwato.

Facebook Forum

XS
SM
MD
LG