Manchester United Ta Sayar Da Adnan Januzaj Fam Miliyan £9.7

A cigaba da saye da sayarwa da akeyi na 'yan wasan kwallon kafa na duniya kungiyar kwallon kafa ta Real Madrid ta bukaci Manchester United, tayi sauri ta kammala cinikn dan wasan gabanta Alvaro Morata, kafin a fara European Champion, don itama ta sayo Kylian MBappe daga Monaco.

Barcelona tana zawarcin tsohon dan wasan tsakiya na Tottenham Evergrande dan shekara 28 da haihuwa dan kasar Brazil, Manchester United ta amince da ta sayarda dan wasanta Adnan Januzaj, ga kungiyar kwallon kafa ta Real Sociedad akan kudi fam miliyan £9.7

Liverpool na gab da kammala sayen Mohammed Salah dan shekaru 25 da haihuwa daga Roma akan kudi fam miliyan £39.

Mai horas da kungiyar kwallon kafa ta Manchester United Jose Mourinho ya bukaci Manchester tayi gaggawar kammala saye dan wasan tsakiya na Inter Millan Pericis kafin a fara Pre-season.

Your browser doesn’t support HTML5

Manchester United Ta Sayar Da Adnan Januzaj Fam Miliyan £9.7