Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Jose Mourinho Ya Musanta Zargin Kin Biyan Haraji


Mai horas da Kungiyar kwallon kafa ta Manchester United Jose Mourinho yace bashi da wata masaniyar zargin da hukumomin kasar Spain suke masa na kin biyan haraji a kasar.

Kasar ta Spain dai tace tana zargin Mourinho, da rashin biyan harajin da yakai kudi yuro miliyan €3.3 kimanin fam miliyan £2.9 kwantankwacin dalar Amurka, $3.6 a lokacin yana matsayin mai horas da kungiyar kwallon kafa ta Real Madrid, dake Spain a shekara 2011 zuwa 2012.

Bayanai da suke fitowa daga bakin wakilinsa yace shi har yanzu bai ga wata takarda dake da alaka da wannan tuhumarba

Mai binciken yace tuni suka gabatar da korafinsu a gaban wata karamar kotu dake Spain, don gurfanar da wanda ake zargin

Sai dai bayanan da sukas fito ta bangaren Mr Mourinho, na nuni da cewar José ya biya kimanin yuro miliyan €26 kimanin Kashi 41% na kudin harajinsa a kasar Spain, na tsawon shekaru ukku da yayi yana kasar a matsayin mai horas da Kungiyar Real Madrid, kamar yadda dokar Kasar ta tanadar.

please wait

No media source currently available

0:00 0:03:05 0:00

  • 16x9 Image

    Ibrahim Jarmai

    Ibrahim Jarmai, ma’aikacin jarida (International Broadcaster Multi Media) a sashen Hausa na muryar Amurka, mai gabatar da shirye shirye a radio da talabijin, da kuma shafukan yanar gizo, dan asalin jihar Kasina.

Facebook Forum

XS
SM
MD
LG