Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

An Fidda Jaddawalin Teburin Firimiya Lig Na Kasar Ingila


Hukumar dake kula da wasan Firimiya lig ta kasar Ingila ta fitar da jaddawalin teburin gasar Firimiya lig na bana 2017/18, kamar yadda aka sani kungiyoyi ashirinne suke fafatawa a gasar ana kuma farawane a tsakiyar watan Augusta kowace shekara.
Ga yadda wasannin zasu kasancene a ranar farko 12/8/2017:

Mai rike da kambun Firimiya a yanzu haka Kungiyar Chelsea, zata kara da Burnley, Sai Arsenal da Leicester City

Sabuwar haurowa gasar Firimiya Brighton da Hove Albion zata kara da Manchester City, Crystal palace da Huddersfield Town, Everton da Stoke City

Manchester United zata gwabza da Westham United, sai Newcastle da Tottenham Hotspur akwai Southampton da Swansea, Watford da Liverpool,
Westbromwich da Bournemouth.

Dukka wasannin za'a bugasune da misalin karfe hudu na yamma agogon Najeriya Nijar Kamaru da kasar Chadi.

Daganan kuma sai wasa ya cigaba harzuwa karshen wasannin na bana.

please wait

No media source currently available

0:00 0:03:57 0:00

  • 16x9 Image

    Ibrahim Jarmai

    Ibrahim Jarmai, ma’aikacin jarida (International Broadcaster Multi Media) a sashen Hausa na muryar Amurka, mai gabatar da shirye shirye a radio da talabijin, da kuma shafukan yanar gizo, dan asalin jihar Kasina.

  • 16x9 Image

    Bala Branco

    Bala Branco ma'aikacin jarida ne a Albarka Radio FM Bauchi dake tarayyan Najeriya wanda yake shirya wa Dandalin VOA labaran wasanni, Haifaffen Unguwar Nufawa ne dake birnin Bauchi. Mazaunin Bauchi a Najeriya.

Facebook Forum

XS
SM
MD
LG