Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Hada Hadar Zaratan 'Yan Wasan Kwallon Kafa Na Duniya


A cigaba da hada hadar ‘yan wasan kwallon kafa da akeyi a yanzu haka dan wasan gaba na kasar Faransa mai taka leda a kungiyar Atletico Madrid Antoine Griezmann ya sake rattaba hannun a kungiyarsa ta Atletico har zuwa shekara 2022.

Zlatan Ibrahimovic mai shekaru 35 da haihuwa ya fara tattaunawa da kungiyar kwallon kafa ta LA Galaxy na kasar Amurka domin mai yuwar ya koma kungiyar da taka leda idan tattaunawar tayi kai.

Dan wasan gaba na kungiyar Liverpool Philippe Coutinho mai shekaru 25 da haihuwa yace akwai rikita rikita bisa harsashe da akeyi na komawarsa Kungiyar Barcelona.

Shi kuwa Alexis Sanchez na Arsenal ya nuna shakkunsa na komawarsa kungiyar Manchester City saboda wasu dalilai dan wasan yace yafi dacewa da ya Koma Bayern Munich.

Dan wasan gaba na Chelsea Diego Costa na shirye shiryen Komawa Kungiyar Atletico Madrid a matsayin aro zuwa tsakiyar kakar wasan badi domin ya dawo da martaban kulob din ganin halin da ta shiga na rashin sayen ‘yan wasa da aka hanata.

Kungiyar kwallon kafa ta PSG dake kasar Faransa ta shaida wa Barcelona da ta cire ranta wajan sayan Marco Verratti domin ba na sayarwa bane ko da nawa zata saya.

Barcelona dai ta saka yuro miliyan €100 don ganin ta sayo dan wasan.

please wait

No media source currently available

0:00 0:03:22 0:00

Facebook Forum

XS
SM
MD
LG