Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Ana Shirin Kammala Ciniki Tsakanin Manchester United Da Real Madrid


A cigaba da hada hadar saye da sayarwa da akeyi na 'yan wasan kwallon kafa ta duniya, yanzu haka kungiyar kwallon kafa ta Manchester United, ta kammala sayen dan wasan baya na Benfica, mai suna Victor Lindelof, a kan kudi fam miliyan 31.

A na shirin kammala ciniki tsakanin kungiyar Manchester United, da Real Madrid, kan sayen dan wasan Real, Alvaro Morata, a sati mai zuwa kan kudi fam miliyan 65.

Kungiyar Barcelona, ta sayi Marlon Santos, dan shekaru 21 daga Fluminense, na tsawon shekaru uku, Roma tace ya zamo dole Liverpool, ta biya fam miliyan 35.5 idan har tana son sayen dan wasanta Mohammed Salah.

Corentin Tolisso, ya Koma Bayern Munich, daga kungiyar Lyon, a kan kudi yuro miliyan 41.5. Westham tana zawarcin mai tsaron raga na kasar Ingila, maisuna Joe Hart a matsayin aro.

please wait

No media source currently available

0:00 0:02:49 0:00

  • 16x9 Image

    Ibrahim Jarmai

    Ibrahim Jarmai, ma’aikacin jarida (International Broadcaster Multi Media) a sashen Hausa na muryar Amurka, mai gabatar da shirye shirye a radio da talabijin, da kuma shafukan yanar gizo, dan asalin jihar Kasina.

  • 16x9 Image

    Bala Branco

    Bala Branco ma'aikacin jarida ne a Albarka Radio FM Bauchi dake tarayyan Najeriya wanda yake shirya wa Dandalin VOA labaran wasanni, Haifaffen Unguwar Nufawa ne dake birnin Bauchi. Mazaunin Bauchi a Najeriya.

Facebook Forum

XS
SM
MD
LG