Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Manchester United Ta Ware Pam Miliyan 183 Akan Cristiano Ronaldo


Cristiano Ronaldo
Cristiano Ronaldo

A cigaba da saye da sayarwa da akeyi na ‘yan wasan kwallon kafa na duniya Kungiyar kwallon kafa ta Manchester United tace zata biya fam miliyan 183 ta kuma hada da mai tsaron ragarta David De Gea wa kungiyar Real Madrid domin domin ta karbi ‘yan wasan biyu Cristiano Ronaldo da kuma Alvaro Morata.

A satin da ya wuce ne Ronaldo ya bayyana wa duniya cewar zai bar kungiyarsa ta Real Madrid sakamakon matsin lambar da hukumar kasar Spain takeyi masa na tuhumarsa da rashin biyan haraji na kimanin fam miliyan 14, wanda wannan dan wasan yace shi baida masaniyar haka.

Ronaldo dai ya Koma kungiyar Real Madrid ne a shekara 2009 daga Manchester Unitet akan zunzurutun kudi fam miliyan 80.

A yanzu haka dan wasan ya sake rattaba hannun wa kungiyar ta Real har na tsawon shekaru biyar inda zai kammala a 2021.

Kocin kungiyar ta Real Madrid Zinadine Zidane na kokarin shawo kan dan wasan ya janye batunsa na barin Real Madrid.

Kungiyar kwallon kafa ta Chelsea tana shirin dawo da tsohon dan wasanta Romelu Lukaku daga Everton.

Barcelona tana yunkurin ganin ta saye dan wasan Everton mai suna Gerard Deulofeus, Arsenal ta shiga sahun zawarcin Carlos Bacca, ita kuwa Westham tana neman Olivier Giroud daga kungiyar Arsenal.

please wait

No media source currently available

0:00 0:04:22 0:00

Facebook Forum

XS
SM
MD
LG