A karon farko cikin shekaru 10, za a fafata a babban wasa na El-Classico tsakanin Real Madrid da abokiyar hamayyatar Barcelona ranar Lahadi mai zuwa ba tare da shahararrun 'yan-wasanna Cristiano Ronaldo da Lionel Messi ba.
Wannan wasan zai iya zama ma'aunin kwazon kowacce kungiya, a tsakaninsu ba tare da tauraronsu ba, duk da dai dama Madrid tana fama da rashin samun nasara a wasannita da ta buga a baya bayannan, tun bayan sauya shekar da dan wasanta Ronaldo ya yi zuwa Kungiyar Juventus a bana.
Rabon da aga kungiyoyin biyu su fafata ba tare da wadannan zakakuran ‘yan wasa ba tun a shekarar 2007 kafin zuwansu kungiyoyin biyu masu hamayya da juna.
Baban wasan Classico na zuwa ne a dai-dai lokacin da mai horas da Kungiyar Madrid Julen Lopetegui ke ci gaba da shan suka game da rashin nasarar da kulob din ke fama da shi, kusan wasanni 5 da ta fafata duk kuwa da matsayinta na mai rike da kambun zakarun Turai.
Kididdiga ta nuna cewa Real Madrid ta buga wasa na tsawon sa’o’i 8.1 ba tare da ta zura kwallo ba.
Ku Duba Wannan Ma Mesut Ozil Ya Kafa Tarihi a Duniyar TamaulaSai dai wasan da ta buga ranar Talata ta dan yi rawar gani wajen zura kwallaye biyu a ragar Viktoria Plzen, a gasar rukuni na cin kofin zakarun nahiyar Turai na banaduk dadai Victoria ta kusa farkewa dab da kammala wasa inda aka tashi ci 2 da 1.
Bayan haka wasan na ranar Lahadi zai zo a dai-dai lokacin da abokiyar hamayyanta wato Barcelona ke ci gaba da haskakawa duk da rashin
kyaftin dinta Lionel Messi, wanda yanzu haka ya ke fama da jinya bayan samun rauni a hannusa, a wasan da kulob din ta lallasa Sevilla da ci 4-2 bangaren Laliga, inda yanzu haka Barcelona take saman teburin La Liga
da maki 18.
Real Madrid za ta yi tattaki ne zuwa gidan Barcelona don fafatawa a wasan farko na El-Classico.