Jaddawalin Rukunin Zagaye Na Biyu Na Gasar Cin Kofin Zakarun Nahiyar Turai

A yau talata za'a dawo cigaba da fafatawa a wasan kwallon kafa bangaren gasar cin kofin zakarun Nahiyar Turai, UEFA Champions League, na shekarar 2017/18 a matakin wasan rukunin zagaye na biyu.

A yau kungiyoyi goma sha shida zasu kece raini a tsakaninsu, daga rukuni hudu kamar haka;

A rukunin (E)

Sevilla zata karbi bakuncin Liverpool, sai Spartak Moscow su kara da Maribor,

A rukunin (F)

Manchester City zata barje gumi da Feyenoord, sai kuma Napoli ta fafata da Shakhtar Donestk,

Sai kuma rukunin (G) inda Monaco zasu marabci RB Leipzig, sai Besiktas da FC Porto,

A rukunin (H) kuwa

Apoel Nicosia zasu karbi bakuncin masu riki da kambun Turai Real Madrid, sai a kara tsakanin Borussia Dortmund da kungiyar Tottenham,

Za'a buga wadannan wasanni ne da misalin karfe tara saura kwata na dare agogon Najeriya, Nijar, Kamaru da Kasar Chadi.

Your browser doesn’t support HTML5

Jaddawalin Rukunin Zagaye Na Biyu Na Gasar Cin Kofin Zakarun Nahiyar Turai