Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Tsofaffin 'Yan Wasan Kwallon Kafa Sun Tuna Baya


'Yan Wasa
'Yan Wasa

A cigaba da wasannin cin kofin Dogarin gwamnan jihar Bauchi, DSP Adamu Ahmed, Mai taken (Aide-De-Camp) da yake gudana a cikin garin Bauchi na tarayyar Najeriya, ya tara tsofaffin 'yan wasan kwallon kafa da suka haura shekaru arba'in da biyar tuna baya.

Inda ake matakin wasan rukuni a ranar Asabar da ta gabata an gwabza wasani tsakanin kungiyar tsofaffin ‘yan wasan kwallon kafa na Young Babies, da Flamingo Old timers, inda suka tashi kunnen doki 1 da 1.

Kungiyar kwallon kafa na General Muhammadu Buhari FC, (PMB Boys) ta sha kashi a hannun Eleven Planners da ci 3-1.

A ranar lahadi kuwa Bauchi Club Old Stars, sun lallasa Horse Power FC, da kwallaye 3-0, sai kuma Dawaki Old Stars ta sha kashi a hannun Bakari Dukku Old Stars da kwallaye 2-1.

  • 16x9 Image

    Bala Branco

    Bala Branco ma'aikacin jarida ne a Albarka Radio FM Bauchi dake tarayyan Najeriya wanda yake shirya wa Dandalin VOA labaran wasanni, Haifaffen Unguwar Nufawa ne dake birnin Bauchi. Mazaunin Bauchi a Najeriya.

Facebook Forum

XS
SM
MD
LG