Jaddawalin Wasannin European League Na Dab Da Na Kusa Da Na Karshe

An fitar da jaddawalin wasan dab da na Kusa da na karshe wato (Quarter Final) na gasar cin kofin Europa league na shekara 2017/18 inda kungiyoyin kwallon Kafa goma sha shida na yankin turai zasu gwabza a tsakaninsu.

Ga yadda wasannin zasu kasance

Kungiyar AC Milan zata kara da Arsenal

RB Leipzig da Zenit,

CSKA Moscow da Lyon,

Sporting Lisbon da Viktoria Plzen,

Borussia Dortmund da Salzburg,

Marseille da Athletic Bilbao,

Sauran kuwa sun hada da Lazio da Dynamo Kiev, sai kuma Atletico Madrid da Lokomotive Moscow. Za'a fara wasan ranar Alhamis 8/3/2018 daga bisani ayi wasa na biyu ranar Alhamis 15/3/2018.

Your browser doesn’t support HTML5

Jaddawalin Wasannin European League Na Dab Da Na Kusa Da Na Karshe