Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Hose Mourinho Ya Bada Tabbacin Fafatawar Pogba


Mai horas da Kungiyar kwallon Kafa ta Manchester united, Jose Mourinho, ya bada tabbacin cewar dan wasan tsakiyar kulob din Paul Pogba, na cikin jerin ‘yan wasan sa da zasu fafata da kungiyar kwallon Kafa ta Sevilla, dake kasar Spain, a gasar cin kofin zakarun nahiyar turai zagaye na goma sha shida, karawar farko wadda za'ayi yau laraba.

Dan wasan dai bai samu damar fafatawa a wasan da Manchester ta yi da Huddersfield town, ba a gasar cin kofin kalubale na kasar Ingila wanda suka sha 2-0 sakamakon gajeruwar rashin lafiya da ya yi fama da ita a satin.

Mai horas da kungiyar kwallon Kafa ta Chelsea, Antonio Conte, ya ce yana da karfin guiwar cewa tawagar sa zasu nuna kwazon su a wasan da zasu yi na biyu da takwarar us Barcelona, a gasar cin kofin zakarun turai a can kasar Spain ranar 14 Maris, inda a haduwar su ta farko aka tashi canjaras 1-1 a gidan Chelsea.

A shekara 2011/12, Chelsea, ta samu nasara a kan Barcelona, a wasan zakarun nahiyar turai inda ta je Camp Nou ta yi 2-2 daga bisani ta ci rata da 3-2.

Kungiyar Arsenal ta tura tawagar ta domin su gane mata dan wasan Bayern Munich mai suna Oguzhan, dan shekara 24, a wasan da Bayern Munich ta yi da Besiktas, Sai dai dan wasan bai buga wasan da kungiyar sa ta sha 5-0 ba.

please wait

No media source currently available

0:00 0:04:58 0:00

  • 16x9 Image

    Bala Branco

    Bala Branco ma'aikacin jarida ne a Albarka Radio FM Bauchi dake tarayyan Najeriya wanda yake shirya wa Dandalin VOA labaran wasanni, Haifaffen Unguwar Nufawa ne dake birnin Bauchi. Mazaunin Bauchi a Najeriya.

  • 16x9 Image

    Ibrahim Jarmai

    Ibrahim Jarmai, ma’aikacin jarida (International Broadcaster Multi Media) a sashen Hausa na muryar Amurka, mai gabatar da shirye shirye a radio da talabijin, da kuma shafukan yanar gizo, dan asalin jihar Kasina.

Facebook Forum

XS
SM
MD
LG