Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Borussia Dortmund Na Duba Yuwuwar Sayen Dan Wasan


Kungiyar kwallon Kafa ta Borussia Dortmund ta kasar Jamus, tana duba yuwuwar sayen dan wasan gaba na Chelsea Batshuayi a matsayin dindindin mai makon aro da yake a yanzu.

Dan wasan dai ya komo kungiyar ta Borussia Dortmund ne a watan Janairun nan da tawuce a matsayin aro inda ya maye gurbin dan wasan ta Aubameyang da ya koma Arsenal.

Batshuayi ya jefa kwallaye biyar a wasanni uku da ya buga wa kungiyar, ciki harda wasan da sukayi a ranar alhamis na gasar European League tsakaninsu da Atlanta inda suka doke kungiyar Atlanta da ci 3-2, dan wasan Batshuayi shi ya jefa kwallaye biyu a cikin uku da suka ci a wasan.

Sai dai a baya ba batun yarjejeniya kan cinikin dindindin da akayi da kungiyar ta Chelsea amma shugaban kungiyar ta Dortmund yace akwai yuwuwar duba tsayuwar dan wasan ganin yadda yake cin kwallaye a duk wasannin da ya buga.

Dan wasan ya taho Chelsea ne daga kungiyar Marseille a shekara 2016 akan kudi fam miliyan £33.1.

please wait

No media source currently available

0:00 0:03:40 0:00

  • 16x9 Image

    Bala Branco

    Bala Branco ma'aikacin jarida ne a Albarka Radio FM Bauchi dake tarayyan Najeriya wanda yake shirya wa Dandalin VOA labaran wasanni, Haifaffen Unguwar Nufawa ne dake birnin Bauchi. Mazaunin Bauchi a Najeriya.

Facebook Forum

XS
SM
MD
LG