Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Abun Alfahari Ne Ka Samu Magaji


Didier Drogba
Didier Drogba

Isaac Drogba mai shekaru 17, da haihuwa dan shahararren dan wasan kwallon kafa na duniya watau Dider Drogba, ya rattaba hannu a tsohowar kulob din da mahaifinsa ya yiwa wasa kungiyar kwallon Kafa ta Guingamp ta kasar Faransa.

Dama ance kyawu dan ya gaji mahaifinsa Isaac Drogba shima dan wasan gabane kamar mahaifinsa, kafin zuwansa kolub din Isaac Drogba ya halarci makaratan koyon kwallon kafa ta Chelsea mai suna Chelsea academy a turance.

Drogba yayi wasa a kungiyar Guingamp daga bisani ya dawo kungiyar Marseille, kafinnan ya koma Chelsea da taka leda a shekara 2004.

A lokacin da yake taka ledarsa a Kungiyar ta Guingamp Drogba ya jefa kwallaye 24 a wasanni 50 da ya buga wa kungiyar.

  • 16x9 Image

    Bala Branco

    Bala Branco ma'aikacin jarida ne a Albarka Radio FM Bauchi dake tarayyan Najeriya wanda yake shirya wa Dandalin VOA labaran wasanni, Haifaffen Unguwar Nufawa ne dake birnin Bauchi. Mazaunin Bauchi a Najeriya.

Facebook Forum

XS
SM
MD
LG