Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Shi Kade Ya Danna Har Guda Uku


Sadio Mane
Sadio Mane

Shahararren dan wasan kwallon kafar nan na Liverpool, kuma da asalin kasar Senegal Sadio Mane, ya samu shiga cikin fitattun ‘yan wasan kwallon kafa na mako a gasar zakaru Turai bayan da ya jefa kwallaye uku a wasan da suka buga da Porto a daren jiya.

Haifaffen kasar Senegal din shi ya jefa kwallon farko dana uku da na biyar a wasan da aka tashi Liverpool ta lallasa Porto, da kwallaye biyar da nema.

Sadio Mane, ya kasance wanda ya fi kowa taka leda a wasan da suka buga jiya.

Sauran wadanda suke cikin fitattun ‘yan wasan sun hada da Ilkay Gundogan, na Manchester City, Christian Erikan, na Tottenham da kuma Marcelo na kungiyar Real Madrid.

Magoya bayan Liverpool suna iya zaben dan wasan da suka ga cewa yafi cancanta.

Facebook Forum

XS
SM
MD
LG