Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Real Madrid Ta Bukaci Thibaut Courtois Ya Jinkirtta Sabunta Kwantiragin Sa


Kungiyar kwallon Kafa ta Real Madrid, ta bukaci mai tsaron raga na Chelsea, Thibaut Courtois, dan shekaru 25 da haihuwa da yayi jinkiri wajan sabunta kwantirakinsa a kungiyar ta Chelsea har zuwa watan Afirilu, domin ta samu damar ganin yuwuwar dauko shi ko kuma David de Gea na Manchester united.

Mai horas da Kungiyar Manchester united, Jose Mourinho ya ce sun gamsu da wasan da Paul Pgoba ya yi a jiya a wasansu da Kungiyar Sevilla a gasar cin kofin zakarun nahiyar turai da aka tashi canjaras 0-0.

Pgoba wanda ya shigo wasan a mintuna na 17 ya maye gurbin Ander Herrera wanda ya samu rauni a wasan.

Mourinho ya ce bayan da dan wasan Paul Pgoba, ya shigo yana yin wasan ya canza bisa kukarinsa.

Wakilan dan wasan tsakiya na Manchester united Paul Pgoba, ya ce kofa a bude take ga manyan kungiyoyin kwallon Kafa na turai ga duk wace take son sayensa.

Kungiyoyin kwallon Kafa na kasar faransa guda hudu ne suke zawarcin dan wasan gaba na Real Madrid, Karim Benzema, cikin kungiyoyin a kwai Lyon, da kuma Paris Saint-Germain.

Maihoras da kungiyar Arsenal Arsene Wenger ya bukaci danwasan gaban kungiyar Danny Welbeck, dan shekaru 27 da haihuwa, da ya sabunta kwantirakinsa a kungiyar.

please wait

No media source currently available

0:00 0:04:09 0:00

  • 16x9 Image

    Ibrahim Jarmai

    Ibrahim Jarmai, ma’aikacin jarida (International Broadcaster Multi Media) a sashen Hausa na muryar Amurka, mai gabatar da shirye shirye a radio da talabijin, da kuma shafukan yanar gizo, dan asalin jihar Kasina.

  • 16x9 Image

    Bala Branco

    Bala Branco ma'aikacin jarida ne a Albarka Radio FM Bauchi dake tarayyan Najeriya wanda yake shirya wa Dandalin VOA labaran wasanni, Haifaffen Unguwar Nufawa ne dake birnin Bauchi. Mazaunin Bauchi a Najeriya.

Facebook Forum

XS
SM
MD
LG