Hira Da Mawaki Mudassir Kasim

Mudassir Kasim

A wannan makon dandalin voa ya sami bakuncin shahararren mawakin nan mai suna Mudassir Kassim wanda ya shafe kusan shekaru ashirin yana sana’ar waka, kuma ya bayyana cewar shi’awa ce ta sa har ya fara waka, kuma ya kara da cewa yawanci mawaka kan fara waka ke a lokacin da suke cikin kuruciya.

Mawakin ya ce mutum bazai san cewar akwai gudummuwar da zai iya bada wa ba sai ya fara wannan harka sa’annan zai iya gane shin wacce irin rawa zai iya takawa wajan ciyar da al’uma gaba da sauran abubuwa makamantan su.

Mudassir ya ce a burin sa na rayuwa, yana matukar jin dadi musamman idan ya raira waka mai ma'ana da zata amfani al'uma baki daya.

Daga karshe ya ce yana wakokin film da soyayya harma a wasu lokuta yakan hada da na siyasa.

Ga cikakkiyar hirar.