Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Kano Pillars Tayi Laga Laga Da Shooting Stars


Tambarin Kano Pillars
Tambarin Kano Pillars

Hukumar gudanarwa ta kungiyar wasan kwallon kafa ta Shooting Stars, ta nemi gafara daga magoya bayanta.

Hukumar dai ta nemi wannan gafara ne biyo bayan abin kunyar da ya faru a filin wasa na Sani Abacha dake birnin Kano, inda kungiyar Kano Pillars, tayi laga laga dan kungiyar shooting stars da ci rututu har shida da babu.

Wani jami’in , na hukumar gudanarwa na kungiyar ta Shooting stars, Jubril Arolowo , yace lalle wannan abin baiyi dadi ba amma ya zama wajibi, a shige wanna babi na rashin samun nasara domin a kuri gaba.

Ya kara da cewa muna matukar baiwa magoya bayamu hakuri na wanna rashin nasara da fatar sun hakura da kuma daukar matakai na kokarin hana afkuwar irin wannan nan gaba.

Yace babu wani mugun tunani kan koci Kadiri Ikhana, sai dai kawai tunanin mafita da hana afkuwar haka nan gaba.

XS
SM
MD
LG