Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Shugaban Kamfanin Saida Jarirai A Kasar India Ya Shiga Wani Hali!


Jami’an ‘yan sanda sun samu damar kama wani shugaban Asibiti, mai suna Arun Bhadoria, an kama shi da zargin saida jarirai a asibitin shi. A duk lokacin da mace tazo asibitin shi da niyar zubar da ciki, sai su bama ‘yan matan shawara kan cewar kada su zubar da cikin.

Su bari idan suka haifi yaran zasu siyar da yaran ga iyaye da basu taba samun haihuwa ba, akan kudi dallar Amurka $1,400 dai-dai da naira dubu dari uku N300,000. Wannan asibitin na gundumar Gwailor, a kasar India, sun bayyanar da kimanin yara biyar da suka siyar ga wasu mabukata.

Asibitin nada jami’ai a cikin garin, da suke yawo lungu da sako don gano mata dake da cikin da basu da bukatar shi, sai su yaudare su da cewar kada su zubar da cikin, wanda daga bisani zasu basu kudi masu yawa. Yanzu haka dai ana tuhumar ma’ikatan asibitin da hukuncin bautar da yara.

  • 16x9 Image

    Yusuf Harande

    Yusuf Aliyu Harande, dan jaridar sashen Hausa na gidan radiyon Muryar Amurka (VOA). Dan asalin Hiliya a karamar hukumar Tambuwal, jihar Sakkwato.

XS
SM
MD
LG