Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

An Zarge Ta Da Cin Zarafin 'Yar Ruko


Wata baiwar Allah da ta karbi 'yar ruko mai shekaru uku da haihuwa wadda a yanzu haka ake zargin ta da cin zarafin wannan karamar yarinya wadda lamarin ya kaiga gurfanar da ita a ofishin 'yan hisba dake jahar Kano.

Ita dai wannan mata da aka sakaya sunanta ta dauki karamar yarinyar ne a matsayin 'yar ruko, amma kamar yadda masu iya magana suka ce, zuciya bata da kashi musamman yadda take sa wasu cikin halin da na sani.

Kamar yadda rahotannin suka bayyana, ita dai wannan mata ta jefar da yarinyar ne inda ta kaiga karya mata cinya a sakamakon haushin wanke mata bayan dari da tayi wanda ya bata ma matar rai.

An gurfanar da matar ne a ofishin 'yan hisba da ke jahar Kano domin jin ba'asin ta dangane da wannan aika aika da makwabtan ta suka bayyanawa 'yan hisba cewar matar ta aikata.

Matar ta nemi karyata zancen amma da shike wadanda suka kai karar sun ce ta dade tana kwatanta irin wannan muun hali, kuma a matsayin su na makwabtan ta dole ne su nemi sa hannun hukuma cikn lamarin doimn fita hakkin makwabtaka.

Ga cikakken rahoton.

  • 16x9 Image

    Ibrahim Jarmai

    Ibrahim Jarmai, ma’aikacin jarida (International Broadcaster Multi Media) a sashen Hausa na muryar Amurka, mai gabatar da shirye shirye a radio da talabijin, da kuma shafukan yanar gizo, dan asalin jihar Kasina.

XS
SM
MD
LG