Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Tsohon Mai-tsaron Gidan "Super Eagle" Ya Samu Karramawa Ta Musamman!


Tsohon mai tsaron gidan kungiyar kwallon kafar Najeriya “Super Eagle” Vincent Enyeama, ya shiga cikin jerin sunayen mutane goma, shahararrun masu tsaron gida na kasashen Turai, na shekarar 2015 da 2016, hakan ya fito ne daga wata kungiya mai lura da harkokin kwallo a kasar “Switzerland.”

Lambar yabon ta zo ne bayan la’akari da akayi akan irin yawan kwallayen da ya kama a cikin mintoci kadan, da yawan kare kwallo daga shiga raga, a ko wane wasa, da dai makamanta kokari irin hakan.

Mai tsaron gidan Vincent, nada shekaru taltin da uku da haihuwa, ya shiga cikin jerin sunayen wasu shahararrun inda ya zamo mutun na tara a jerin sunayen fitattu. Dan wasan dai ya buga wasan kasa-da-kasa, wanda a shekarar da ta gabata ne ya sanar da cewar zai bar wasa.

  • 16x9 Image

    Yusuf Harande

    Yusuf Aliyu Harande, dan jaridar sashen Hausa na gidan radiyon Muryar Amurka (VOA). Dan asalin Hiliya a karamar hukumar Tambuwal, jihar Sakkwato.

XS
SM
MD
LG