Cristiano Ronaldo Ya Cika Wasanni 50 Da Kwallaye Uku A Kowane

Shahararen dan wasan kwallon Kafa na duniya dan kasar Portugal, wanda yake taka leda a kungiyar Real Madrid Cristiano Ronaldo, ya cika lisafin wasannin hamsin yana samun nasarar jefa kwallaye uku a kowane wasa da ya buga wa kungiyar Real Madrid, wato (Hat-trick) a turance.

Dan wasan ya samu wannan nasara ne a ranar lahadi 18/3/2018, yayin da suka doke Girona da ci 6-3 a gasar Laliga mako na 29 inda ya jefa kwallaye hudu daga cikin shida da Real ta sha.

A yanzu haka dai Cristiano, ya zurara kwallaye 37 a wasannin da ya buga wa kungiyar ta Real Madrid, a wannan shekarar inda a Laliga yake matsayi na uku a yawan jefa kwallaye tare da kwallaye 21.

Kuma kungiyar ta Real Madrid, tana mataki na uku ne da maki 60 a teburin Laliga a wasan mako na 29 Atletico Madrid, tana samanta da maki 64 sai Barcelona, a mataki na daya da maki 75. saura wasanni takwas a kammala gasar ta Laliga na bana.

Your browser doesn’t support HTML5

Cristiano Ronaldo Ya Cika Wasanni 50 Da Kwallaye Uku A Kowane