Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Kungiyoyi Da Dama Sun Fara Nuna Ra'yoyin Su Kan Wasu Fitattun 'Yan Wasa


Kocin kungiyar kwallon Kafa ta Everton, Sam Allardyce ya ce yana da shi'awar dauko dan wasan baya na Manchester united, Phil Jones, mai shekaru 26, da haihuwa in har shine zai cigaba da rike jagoranci a kungiyar a tsawon shekara mai zuwa.

Har ila yau kungiyar Everton, tana kokarin ganin ta dauko dan wasan tsakiya na Arsenal, Jack Wilshere, a matsayin kyauta a karshen kakar wasan bana. Manchester City, na iya sayen dan wasan tsakiya na Shakhtar Donestk mai suna Fred, 25 wanda ita ma Manchester united ta nuna shi'awarta kan dan wasan.

Kungiyar kwallon Kafa ta Liverpool, tana duba yuwuwar dauko dan wasan gaba RB Leipzig na kasar Jamau mai suna Timo Werner, dan shekaru 22 da haihuwa a karshen kakar wasan bana da zarar an bude hada hadar ‘yan wasa.

Shugaban kungiyar kwallon Kafa ta Arsenal, Ivan ya ce yana da bukatar Kocin kungiyar Juventus, Allegri yazo ya maye gurbin Kocin kungiyar ta Arsenal Arsene Wenger da zarar ya bar kungiyar.

Dan wasan gaba na Atletico Madrid, Antoine Griezmann, mai shekaru 26 a duniya ya fara neman gidan zama a Catalan domin shirye shiryen sa na komawa kungiyar kwallon Kafa ta Barcelona.

Arsenal da Napoli da kungiyar Roma sun jera sahu guda kan zawarcin mai tsaron raga na Toulouse mai suna Alban Lafon.

please wait

No media source currently available

0:00 0:04:38 0:00

  • 16x9 Image

    Ibrahim Jarmai

    Ibrahim Jarmai, ma’aikacin jarida (International Broadcaster Multi Media) a sashen Hausa na muryar Amurka, mai gabatar da shirye shirye a radio da talabijin, da kuma shafukan yanar gizo, dan asalin jihar Kasina.

  • 16x9 Image

    Bala Branco

    Bala Branco ma'aikacin jarida ne a Albarka Radio FM Bauchi dake tarayyan Najeriya wanda yake shirya wa Dandalin VOA labaran wasanni, Haifaffen Unguwar Nufawa ne dake birnin Bauchi. Mazaunin Bauchi a Najeriya.

Facebook Forum

XS
SM
MD
LG