Dumamar Yanayi Na Barazana Ga Lafiyar Yara A Duniya

Gurbatar yanayi na haddasar da matsaloli da dama, ana iya cewa yaro daya cikin hudu ke mutuwa ‘yan kasa da shekaru 5, a fadin duniya, wanda adadin su ya kai milliyan daya da dubu dari bakwai.

Hukumar kiwon lafiya ta duniya, ta tabbatar da cewar idan har ba’a dauki kwararan matakaiba mutuwar zata karu matuka, idan har ba’a dauki matakan kawo karshen gurbatar yanayi ba.

Hukumar ta gwada matsalolin da gurbatar yanayi ke haifarwa ga yara, da fitar da hanyoyi biyu don magance hankan, a wani bincike da suka gudanar. Mai take “Riko da yanayi mai durewa a duniya” da “Maida hankali ga lafiyar yara da yanayi.”

Burin shine kada a gurbata yanayi, don kariya ga yara da yanayin da jama’a ke rayuwa, don samun lafiya mai inganci. A cewar masana, gurbattacciyar iska da jarirai ke shaka na zama sanadiyyar mutuwar yara sama da milliyan 6.5 a kowace shekara.

Wanda ya hada da yara sama da 600,000 masu shekaru daga daya zuwa biyar na haihuwar su. Margaret Chan, darakta janaral ta hukumar kiwon lafiya ta duniya, ta bayyanar da cewar kananan yara suna cikin hatsari na mutuwa a lokacin da suke da kanana shekaru. Musamman a wannan yanayi na zafi a ake tunkara