Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Za'a Samar Da Hantar Roba Ga Masu Fama Da Ciwon Hanta


Taron likitoci masana na gabatar da wani bincike, don fito da wata hanyar magance cutar sankarar hanta. Ga duk masu dauke da cutar, za’a iya samar musu da hantar roba. Suna ganin cewar idan su kayi hakan, zai ba masu dauke da irin cutar, damar zama kamar sauran mutane.

Mafi akasarin maganin cutar sankarar hanta, shine a dasama mutun wata hantar da akan iya cirowa daga jikin wani mutun. Masana na ganin wannan wata babbar matsala ce, musamman ga duka mutane. Baya ga shan wani magani da zasu rika yi har iya tsawon rayuwar su.

Domin a wasu lokutta hantar da akan dasa ma wasu, bata karbar jikin wasu, wanda hakan yakan iya zama sanadiyar mutuwar mutun biyu a madadin daya, da mai badawa da mai karba. Don haka suna ganin cewar idan suka samar da wata hanya mafi sauki, lamarin sai yafi bada ma’ana.

A cewar Farfesa Kattesh Katti, na jami’ar Missouri, wanda ke jagorantar binciken, ya bayyana yunkurin su na ganin sun saukaka hanyoyin magance manya-manyan cututtuka a duniya. Wanda suka hada da samar da wani magani, da zai yaki cututtukan da kan addabi wasu sassan jikin dan’adam.

  • 16x9 Image

    Yusuf Harande

    Yusuf Aliyu Harande, dan jaridar sashen Hausa na gidan radiyon Muryar Amurka (VOA). Dan asalin Hiliya a karamar hukumar Tambuwal, jihar Sakkwato.

Facebook Forum

XS
SM
MD
LG