Akalla mutane kimanin biyar tare da wani jami’in tsaron ‘yan-sanda sun rasa rayukan su, a yayin wata rigima ta barke tsakanin jami’an tsaro da wasu mambobin kungiyar asiri, tsakanin ranar Litin da jiya Talata.
Haka abun ya ritsa da wasu ‘yan kasuwa mutun biyu, a kasuwar kasa-da-kasa ta Ladipo, biyo bayan hari da aka kaima ‘yan kungiyar ta asiri, rahoto yayi nuni da cewar an daba ma wani mutun wuka wanda yayi sanadiyar mutuwar shi har lahira.
Rikicin dai da ya faru a jiya a anguwar Idi-Oro na birnin Lagos, yayi sanadiyar mutuwar wasu kana wasu da dama sun raunata, fadan da ya kaure ranar Talata da misali karfe 3 na yamma.
Ana tunanin cewa fadan jiya Talata ya biyo bayan arangama tsakanin yan sandan gundumar D, a yankin Muhsin da yan kungiyar asiri, bayan 'yan sandan sun gano inda yan kungiyar asirin ke boyewa.
Jaridar The Nation ta ruwaito cewar sai da yan sanda na mussaman masu kwantar da tarzoma na “Rapid Response Squad” a turance suka shiga lamarin, don kwantar da hankali cikin gaggawa da wasu jami’an tsaro a yankin na Idi-Oro a birnin Lagos.
Facebook Forum