Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Mutanen Da Ake Zargi Da Kisan Dalibin Jami'ar ABU Sun Shiga Hannu


Rundunar ‘yan sandan jihar Kaduna ta cafke wasu mutane biyu da ake zargin da kisan wani dalibin jami’ar Ahmadu Bello, dake Zaria.

Shi dai dalibin yana shekaransa na farko ne a jami’ar inda yake karatu a fanin likitan dabbobi wanda aka kashe a ranar juma’ar da ta gabata.

Kakakin rundunar ‘yan Sandan na jihar Kaduna Mukhtar Aliyu, wanda ya tabbatar da afkuwar lamarin yace rundunar na cigaba da binciken dalilin afkuwar lamarin.

Kakakin ya kara da cewa da zarar an kammala bincike za a gurfanar dasu a gaban kuliya domin fuskantar shara’a.

Facebook Forum

XS
SM
MD
LG