Sabuwar Wayar iPhone X, Ta Wuce Tsara, Wajen Tsarin Kalleni Na Bude

Sabuwar wayar Apple ta iPhone X, zata zama abun kwatance, musamman idan akayi la’akari da yadda sabuwar wayar tazo, da sabon salo wajen budewa. Wayar dai ta share babin amfani da zanen yatsan hannu wajen budewa, ganin cewar zamani ya canza.

Yanzu haka dai mutane zasu iya dai-dai ta samfurin fuskar su wajen tsara yadda suke so wayar ta dinga budewa, batare da wani ya bude wayar ba, batare da ainihin fuskar mai wayar ba.

Mutun zai bukaci kallon wayar sau da dama, kamin wayar ta dauki duk wasu abu da zata bukata a fuskar shi don zama shaida, wasu na’urori a cikin wayar zasu gwada wasu alamu da suke fuskar mutun, da suka kai yawan launuka 30,000.

Wayar dai da kudinta zai fara da kimanin dallar Amurka $1,000 kwatan kwacin naira N360,000. Kudin ta yafi na iPhone 8, da karin dallar Amurka $300. A ranar Juma’a mai zuwa ake sa ran za’a fara siyar da wayar ga wasu mutane kalilan.

Sauran mutane kuwa za’a isar da sakon wayar a gidajen su cikin sati 5-6, duk wanda ke bukatar wayar sai ya buga sammako, zuwa ofisoshin Apple da suke a ko’ina don siya cikin sauri.

Wasu wayoyi na amfani da tsarin kalleni na bude, amma sau da yawa mutane sai sun dinga shiga cikin shafin tsare-tsare na wayar su 'settings' don shaidama wayar fuskar su daga lokaci zuwa lokaci.

Amma tsarin da kamfanin Apple ya fito da shi, da ya wuce na kowa shine, wayar zata iya daukar hoton mutun da ajiye shi a cikin kwakwalwar ta, koda kuwa mutun ya aske gashin fuskar, idan ya kalli wayar zata gane shi.

Wayar nada karfin tuna fuskar mutun ta hanyoyi da dama, ba kawai sai fuskar mutun ta zama iri daya ba akowane lokaci, kamar yadda tsarin zanen hannun mutun yake babu canji.