Facebook, Da Twitter, Da Microsoft, Da YouTube Na Aiki Tare Wajen Dakile Hanyoyin Yada Mummunar Akida

Manyan kamfanonin hanyoyin sadarwa na Amurka da suka hada da Facebook da Twitter da Microsoft da kuma Youtube, na aiki tare domin gina kundin ajiya da binciken hotuna da hotunan bidiyon da ake amfani da su wajen janyo hankulan mutane ko sauya musu tunani domin shiga kungiyoyin ‘yan ta’adda.

Kamfanonin baki daya zasuyi amfani da kundin don samun sauki wajen bincikar duk wasu hotuna da ‘yan ta’adda ke amfani dasu wajen jan ra’ayin matasa da cusa aki’ada ta daban.

A wata sanarwa ta hadin gwiwa da kamfanonin suka kafe sunce, dandalinsu ba guri ne na yada akidojin ta’addanci ba, haka kuma duk lokacin da suka gano wani abu makamancin wannan dabi’a zasu dauki matakan da suka dace dai dai da tsarinsu.

Wannan yunkuri na kamfanonin yazo ne shekara daya bayan da kamfanonin suka hada kai domin su gano da kuma cire fina finan batsa da akayi amfani da kananan yara a ciki daga kan dukkannin kofofinsu.

Cikin wannan shekara dai shafukan sadarwa sun fuskanci suka kan yadda ake ganin basa tabuka komai wajen gano da cire duk wata farfangandar ‘yan ta’adda.

Your browser doesn’t support HTML5

Facebook, Da Twitter, Da Microsoft, Da YouTube Na Aiki Tare Wajen Dakile Hanyoyin Yada Mummunar Akida