Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Zai Kwashe Shekaru Ukku A Gidan Yari Akan Zatar Batirin Mota


Wata kotu mai zama a Ibadan, ta yakewa wani matashi Kehinde Akinpade, mai shekaru talatin da ukku, hukuncin zaman watani ukku, a gidan yari.

Wannan ya biyo bayan samun shi da laifin satar batiran mota biyu a cikin motar da aka ajiye a layin da gidan gidansu yake, a unguwar Akobo a garin Ibadan, da aka kiyasta kudinsu akan Naira 70,00.

An sake yanke masa hukuncin wasu watani ukku, akan cin zarafin wani mai suna Folorunsho Adewuyi, inda yayi amfani da adda.

Mai gabatar da kara Philip Amusan, ya ce Akinpade, ya aikata laifuffukan ne a ranakun 23, da 25, ga watan Nuwamban da ta gabata.

XS
SM
MD
LG