Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Jami'an Super Falcons Zasu Turai Karin Samun Horo In Ji (NFF)


Shugaban hukumar kwallon kafa ta Najeriya, Amaju Pinnick, ya bayyana cewa, jami’an hukumar NFF, masu kula da kungiyar Super Falcons, zasu je Turai, domin samun karin horo akan kwallon kafa.

Shugaban ya furta haka ne a wajan wani liyafa da aka shiryawa kungiyar ta Super Falcons, yana mai cewa zai kan jami’an Turai, domin samun Karin horo.

Ya nuna farin cikinsa ga nasarar da kungiyar ta samu,ya kuma ce masu kula da kungiyar karkashin shugabancin Blessing Omagbemi, suma zasu sami tukwici.

A cewarsa “ ku abin alfaharin mu ne kuma da yardan Allah, zamu biya duk bashin da kuke bin hukumar” ya kara da cewa cin kofin har sau ukku, ba karamin aiki bane ba zamu iya zakamaku ba.

XS
SM
MD
LG