Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Ta Jefa Gawar Danta Mai Shekaru 34, Cikin Magudanar Ruwa


Rundunar ‘yan Sandan Jihar, Legas, ta damke wata mata mai suna Bosede Adekunle, wanda ake zargin cewa ta jefa gawar danta cikin wata magudanar ruwa, a unguwar Ipaja, da Legas.

Mazauna unguwar ne suka gano gawar Kayode Adekunle, mai shekaru talatin da hudu, da ta fara zagwanyewa kwanaki biyar bayan da aka jefar da gawar.

Shi dai wannan matashi yayi fara da rashin lafiya kamar yadda rahotani suka nuna yana fama da cutar farfadiya kuma ya dan jima mahaifiyarsa da kannansa ke jiyarsa a gida, bayan da rai yayi halin sa sai suka daukeshi cikin dare suka jefa shi cikin magudanar ruwar

Gano gawar ke da wuya sai jama’a suka hau dukan mahaifiyarsa daga bisa sai ‘yan Sanda suka ceceta.

Kakakin ‘yan Sandan jihar Legas, SP Dolapo Badmos, wace ta tabbatar da lamarin tace ana ci gaba da bincike akai domin tabbatar da gaskiyar abinda ya faru.

XS
SM
MD
LG