Abin Takaici Ne Yadda Matasa Suka Tsunduma Cikin Shan Kwayoyi- Inji Mu'azzam Umar

Mu'azzam Umar

Mu’azam Umar mawaki da ya shafe shekaru bakwai yana waka, ya ce yanayin rayuwa ne ya sa ya fara waka, mussamam ma halin da matasa suka tsinci kansu na shaye-shaye.

Ya ce ruwan da ya dake ka shine ruwa, a halin da ake ciki matasa basu sami kyakkyawan tushe ba wanda ya jefa yawanci cikin halin ha’ula’I a fannoni na zama koma baya a cikin alumma.

Mawakin ya kara da cewa an bar matasa a baya a harkar demokradiya da harkokin ciyar da kasa gaba, kuma, basu da ta cewa a cikin alu’umma.

Mu’azam ya ce abin takaici ne yadda matsa suka tsunduma cikin harkar shan kwayoyi, bangar siyasa da dukkanin wasu abubuwan da basu dace ba.

A cewarsa ta hanyar waka yana isar da sakonninsa ga matasa domin su gyara rayuwarsu.

Your browser doesn’t support HTML5

Abin Takaici Ne Yadda Matasa Suka Tsunduma Cikin Shan Kwayoyi- Inji Mu'azzam Umar