Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Ina Matukar Son Ci Gaba Da Karatu Koda Na Sakandire Ne - Nji Fiddausi Yako


Fiddausi Yako
Fiddausi Yako

Fiddausi Yako, matashiya mai kimanin shekaru 12, yar asalin karamar hukumar Kiru, ta ce tana zuwa tun daga garin yako domin sayar da gyada a rashin samun damar cigaba da karatun sakandire.

Ta ce ta kammala firamare a Gazam, dake Yako, inda ta kammala aji shida tun daga nan da ta ga lokaci na neman kure mata sai ta fara talla, duk kuwa da cewar ta samu nasara a jarabawarta.

Ta ce tana matukar burin cigaba da karatu koda na sakandire ne domin samun cigaba a rayuwa, kuma ta kara da cewa tana da ra’ayin zama malamar makaranta, domin ko ba komai zata kara wasa kwakwalwarta ta hanyar koyarwa da kuma cudanya da dalibai.

Ko da yake ta ce iyayenta ne ke dora mata tallar gyada, tana yi domin ta sama musu kudi don kashe bukatun yau da kullum.

please wait

No media source currently available

0:00 0:02:15 0:00

  • 16x9 Image

    Ibrahim Jarmai

    Ibrahim Jarmai, ma’aikacin jarida (International Broadcaster Multi Media) a sashen Hausa na muryar Amurka, mai gabatar da shirye shirye a radio da talabijin, da kuma shafukan yanar gizo, dan asalin jihar Kasina.

XS
SM
MD
LG