Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Wani Matashi Sojan Gona Ya Shiga Hannu

Sojojin da ake zargi da kin zuwa Arewa maso gabacin kasar domin yakar masu tsassauran ra'ayin addini sun hallara a gaba kotun Soja a Abuja, 2 ga Oktoba 2014.
Sojojin da ake zargi da kin zuwa Arewa maso gabacin kasar domin yakar masu tsassauran ra'ayin addini sun hallara a gaba kotun Soja a Abuja, 2 ga Oktoba 2014.

Jami’an Sojan Najeriya, na Artillery Brigade, dake Bauchi, sun cafke wani matashi Adam Alexander, mai shekaru ashirin da biyu wanda yayi shigar Sojan gona.

An cafke Alexander, ne a lokacin da yake sanye da khakin Soja, yake kuma kokarin sayarda wani wayar sata.

Kakakin Sojojin Captain Sunday Akinkumi, wanda ya nuna Sojan gonan ga manema labarai saye da khakin Sojoji yace ya addabi mutane da yi masu fashi.

Ya kara da cewa an cafke, Adam Alexander, dan asalin Maiduguri ne a kasuwar Wunti, a lokacin da yake kokarin sayarda wata wayar Samsung Galaxy Note 5 na sata akan kudi Naira dubu saba’in.

XS
SM
MD
LG