Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Wasu Shahararrun Barayi Masu Fashi Da Makami Sun Shiga Hannu


Wani shahararren barawo Alhaji Hodi Adamu, mai fashi da makami wanda ya addabi jama’ar, jihar Adamawa, dubunsa ta cika ya shiga hannun hukuma.

Kakakin ‘yan Sanda Najeriya, mataimakin kwamishinan ‘yan Sanda Don Awunah, ne ya bayyanawa manema labarai a Abuja.

Ya ce bayanan da suka samu daga bakin wanda ake tuhumar shi ya taimakawa jami’an ‘yan Sandan wajan cafke wasu ‘yan fashi Rabo Bello da Oliver Honiol.

Kakakin ya kara da cewa jami’an na ‘yan Sandan Najeriya, sun damke wasu masu fashi da makami masu garkuwa da mutane da wasu ‘yan Sanda hudu masu taimaka masu wajan gudanar da mummunar aikinsu a jihar Kogi.

XS
SM
MD
LG