Cikin jerin kasashen da su kafi zaman lafiya a fadin duniya, a wani rahoton da wata hukumar “Global Peace Index” ta fitar da yayi nuni da cewar, wadannan kasashen anyi amfani da karfin sojojin su ne, da yadda suke amfani da karfin mulki wajen muzgunama ‘yan kasar. Hakan ya bayyanar da su a matsayin kasashe da su kafi zaman lafiya a fadin duniya. Don kuwa gwamnatocin su, suna taiamakama al'umar kasashen.
Sanin kowane cewar, zaman lafiya shine ginshikin rayuwar dan adam, wanda idan babu lafiya babu rayuwa. Sudai wadanna kasashen kamar kasar Germany, tana cikin kasashe masu zaman lafiya a fadin duniya, kana kasar Norway, da kasar Belgium.
Kasar Hungary, sannan kasar Singapore, da kasar Netherlands, haka kasar Poland, nacikin sahu da kuma kasar Mauritius, sai kasar Slovakia, da kasar Spain, kana kasar Croatia, da kasar Chile, sai kasar Botswana, sannan kasar Bulgaria, a karshe kuwa sai kasar Malaysia. Wadannan sune jerin kasashe talatin 30, da akayi ittifakin cewar, sunfi sauran kasashe zaman lafiya a fadin duniya.