NIJER: Kungiyoyi Sun Tallafaw Masu Ketarawa Algeria Da Aka Maido Gida

Yayin da wasu daga cikin masu tafiya yawon bara kasar Algeriya, wadanda yawancin su ke rasa rayukansu a hamadar jamhuriyar Nijer a sakamakon shishin ruwa ke ci gaba da sa rayukansu cikin wannan matsala, Baya bayan nan anyi ta maido da mata da kananan yara zuwa kasar ta jamhuriyar Nijar.

Dalilin haka ne wakiliyar sashen Hausa Tamar Abari ta sami zantawa da wasu daga cikin wadanda aka dawo dasu kasar ta Nijar, kuma sun bayyana cewa sun hakura domin a cewar su, abin da suka dade suna nema yanzu ya samu.

Sun bayyana hakanne a sakamakon tallafin da wasu kungiyoyi suka basu na kudi da dabbobi domin zuba jari.

Wadanda suka ci moriyar wannan tallafi dai sun bayyana cewa daman talauci da rashin ayyukan yi ne suka tursasa su zuwa kasar ta Algeria, kawo yanzu dai gwamnatin jamhuriyar Nijar ta sami nasarar kamo wasu daga cikin 'yan kasar daga Aljeriya.

Rahotanni sun bayyana cewa matasa da dama daga kasashen dake makwabtaka da kasar ta Nijer suke bi ta barauniyar hanya cikin hamada domin ketarawa zuwa kasar Algeriya harma da wasu kasashen turai.