Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Wasu Kungiyoyin Asiri Sun Yi Gumurzu


Matasa
Matasa

Wasu ‘yan kungiyoyin asiri masu gaba da juna sun yi gumurzu a Obiaruku, karamar hukumar Ukwuani a jihar Delta.

Kamar yadda jaridar Vanguard, ta ruwaito matasan sun tada hankalin jama’ar dake zaune a yankin inda abin ya koma kwace inda suka dingi raba mutane da kayayyaki su.

Shi dai wannan rikici an fara shine da gardama a wata mashaya daga bisani ya rikide ya zama fada a cikin gari inda wadanda basu jib a basu gani bay a shafe su.

Daga bisa kuma sun nufi gidan tsohon shugaban ‘yan sintirin yankin inda suka jimasa ciwo.

Kakakin ‘yan Sandan jihar Celestine Kalu, wanda ya tabbatar da afkuwar lamarin yace mutun daya ya rasa ran sa wasu biyu kuma na samu magani a asibiti.

XS
SM
MD
LG