Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Yawancin Furodusoshi Sun Sauya Akala Duba Da Sauye-Sauye A Kannywood


Kamal S Alkali
Kamal S Alkali

Kamal S Alkali, ya ce tun bayan ziyartar DandalinVOA da yayi a baya sabon abin da ya faru da sana’arsa shine ya fito da wani sabon shiri da yayiwa lakabi da "daga jarumanku", sannan ya ce yanzu masu shirya fina finai sun fi mayar da hankali wajan wallafa shiryeshiryensu a tashoshin Youtube.

Ya ce da dama furodusoshin fina-finai sun sauya sheka duba da yadda ake ta samun sauye-sauye a Kannywood, duba da ganin cewar ta nan ma ana samun kudi, ya ce a yanzu babban abinda ya dace shine, wayar da kan masu shirya fim domin tafiya dai-dai da yadda wannan sabuwar kasuwa ta ke.

Kamal, ya ce tabarbarewar kasuwar masana'anta a hannu guda ta dakushe masana'antar, a wani bangaren kuma ya fadada cigaban zamani da tafiyar da yadda duniya take a yanzu.

Shafin youtube, shine shafin da akewa dafifi a yanzu amma sai dai abin dubawa shine, sai mutum na da yawan mabiya ne sannan zai fara samun kudi, muddin jarumi bashi da mabiya toh lallai ba wani alhari da zai samu.

Daga karshe ya bayyana cewa ya shiga gasar Africa viewers award AMVCA, inda ya samu certificate na cancanta wanda a cewarsa wani cigaba ne a bangarensa.

please wait

No media source currently available

0:00 0:05:11 0:00

  • 16x9 Image

    Ibrahim Jarmai

    Ibrahim Jarmai, ma’aikacin jarida (International Broadcaster Multi Media) a sashen Hausa na muryar Amurka, mai gabatar da shirye shirye a radio da talabijin, da kuma shafukan yanar gizo, dan asalin jihar Kasina.

Facebook Forum

XS
SM
MD
LG