Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Masoyan Shahararren Mawaki Davido Sun Durfafe shi


Masu iya magana sun ce a taba kida a taba karatu, kwanaki kadan da suka gabata ne shahararren mawakin nan dan asalin Najeriya, wanda ake kira Davido, kuma mai farin jini ga matasa ya bayyana a shafukan yanar gizo sanye da kayan yiwa kasa hidima wanda aka sani da (NYSC).

Shi dai Davido mawaki ne kuma dan asalin Najeriya, wanda wakokinsa suka sami karbuwa ga matasa a Najeriya da sauran kasashen duniya da dama, wadanda suka hada da masu amfani da harshen Turanci, Faransa da sauran harsuna duk da cewa wakokinsa cikin harshen turanci suke.

Abin mamakin da ya dauki hankalin matasa akan wannan matashin mawaki shi ne, ya yanke shawarar komawa kasarsa ta asali domin yi wa kasa hidima bayan kammala karatun sa na jami'a duk da cewa matashin ya tara dukiya sakamakon alakanta shi da sayen jirgin sama da aka yi watanni kadan da suka gabata duk da cewa ba tabbacin hakan.

A shafukan sada zumunta na yanar gizo, masoya wannan mawaki musamman magoya bayansa sun yi ta tofa albarkacin bakin su musamman wadanda ke gudanar da iri wannan aiki na yi wa kasa hidima da ake biya kudin cin abinci Naira 19,800 a kowane karshen wata cewar "kasancewar sa mai arziki me zai yi da kudin alawus din da za a ba shi? ya basu kawai".

Shi dai wannan mawaki na daya daga cikin mawakan da suka yi suna a duniya, kuma dan asalin Najeriya ne amma bai yi girman kai ba duk da dukiyar da Allah ya bashi, da kuma kasancewarsa wanda yayi karatu a wata kasa kuma ya tara dukiya.

Ya kuke kallon wannan lamari?

  • 16x9 Image

    Ibrahim Jarmai

    Ibrahim Jarmai, ma’aikacin jarida (International Broadcaster Multi Media) a sashen Hausa na muryar Amurka, mai gabatar da shirye shirye a radio da talabijin, da kuma shafukan yanar gizo, dan asalin jihar Kasina.

Facebook Forum

XS
SM
MD
LG