Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Daga Shakiyi Zuwa Kuku- Sabon Salon Mawaki Snoop Doggy


Shaharraren mawakin hip hop na kasar Amurka wanda akafi sani da Snoop Dogg yana gab da fara wani shirin na girke girke wanda za’a rika ganin sa ya nuna korewa wajen dafe dafen abinci daban daban kama daga kaza,kaguwa, jan nama, shatanlalle, da sauran nau’ukan abincin Amurka.

Kamar yadda akasani dai Snoop Dogg mawaki ne kuma mai bada umirni, ya fara nuna ra’ayin sa na girki tun shekarar 2016 inda ya fito cikin shirin Martha Stewart shirin girke girken da akayi wa lakabi da ‘Martha and Snoop’s Potluck Dinner party’.

kamar yadda akasan Snoop Mawaki ne mai rawar kai wanda ake alakanta shi da shaye shaye amma yanzu ga dukkan alamu wannan ra’ayi na girkeke zai iya yin sanadiyar raba shi da tsohuwar rayuwar sa, yanzu haka yana kokarin wallafa littafin sa na farko akan girki wanda ya yiwa lakabi da “ daga shakiyi zuwa kuku wato a turance ( from Crook to Cook).

Domin ci gaba da samun Karin bayani Ku ziyartar shafikan mu na yanar gizo mai adireshi www.dandalinvoa.com da kuma voahausafacebook domin a bayyana ra’ayi.

please wait

No media source currently available

0:00 0:01:32 0:00

  • 16x9 Image

    Daula Saleem

    Daula Saleem, Ma’aikaciyar Jarida ce (International Broadcaster - Multimedia) a Sashen Hausa na Muryar Amurka dake birnin Washington, D.C. Yar asalin Jihar Katsina. Ta karanta aikin Jarida a Jami’ar Bayero University Kano.

Facebook Forum

XS
SM
MD
LG