Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Idris Elba Bakar Fata Na Farko Ya Maye Daniel Craig A Fim Din James Bond 007


Akwai 'yan fim da yawa da za su iya fitowa a fim in James Bond bayan Daniel Craig, da ya sha fitowa yayi ritaya daga abin da ya ki jini. Akwai 'yan wasan fim kamar su Tom Hardy, Michel Fassbender duk da cewa dan asalin kasar Ireland ne, Tom Hiddleston, David Oyelowo wanda shine ke karatu a littafin James bond din. Amma a zahirin gaskiya Idris Elba ne ya kamata ya fito a shirin fim din James Bond nan gaba.

Ana ta jeka ka dawo kan wannan lamari na cewa Elba ya fito a matsayin Bond. Wannan zancen an fara shi ne tun shekarar 2014, da aka saki wasu sakonni ta hanyar email inda a lokacin wanda ake shirya shirin James bond da ita Amy Pascal, ta ce ya kamata a ce Idris Elba ne zai fito a matsayin james bond nan gaba.

Ba wani babban abu bane amma abu ne mai kyau a cewar masu shirya fim din James Bond, suna neman su chanza salon wanda zai fito a matsayin Jarumi Bond wand ba farin fata bane. Idris Elba shine bakar fata na farko da ake sa ran zai fito a shirin fim din James Bond.

  • 16x9 Image

    Ibrahim Jarmai

    Ibrahim Jarmai, ma’aikacin jarida (International Broadcaster Multi Media) a sashen Hausa na muryar Amurka, mai gabatar da shirye shirye a radio da talabijin, da kuma shafukan yanar gizo, dan asalin jihar Kasina.

Facebook Forum

XS
SM
MD
LG