Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Nishadi Da Waka A Tsakanin Matasa Na Kawo Hadin Kai


A yau Dandalin VOA ya samu bakunci wasu gungun mawaka wanda aka fi sani da MKlax - wato Kassim Lawal da IDRIS Yunusa, matasan mawaka da suka hada kansu kuma suka zano gwarzaye a wani shirin da mafi yawan masu shirya fina-finai ke hadawa, na gasar fitar da gwanin dan rawa domin tallata fina-finansu.

Kassim Lawal wanda shine shugaba ya ce masu shirya fina-finan na fitar da gasar ‘1minutes dance competition’ da ke taimaka masu wajen tallata sabon fim din da zasu fitar inda ake saka wannan gasar a shafin yanar gizo.

Wadannan mawaka dai sun ce unguwarsu daya hakan ne yasa abun nasu yazo masu da sauki, ta kai har bayan fice da suka yi ta shafin Instagram, akan gayyace su a unguwarsu da ma na makwabta domin su nishadantar da mutane a lokutan bukukuwa da makamantansu.

Ko da yake Kassim Lawal, yace baya ga harka ta rawa da waka da su ke yi, yana makaranta inda yake karantar aikin jarida a jami'ar Bayero ta Kano. Shi kuwa Idirs Yunusa, cewa yayi al'umma da farko na yi masu kallon 'yan kwaya, ganin cewa abinda matasa suka fi maida hankali akai, kenan a yanzu na harkar shaye-shaye da makamantansu.

Kassim nada burin zama Pilot’ matukin jirgin sama, amma a yanzu ya canza ra’ayi duk abinda Allah ya bashi shine daidai.

please wait

No media source currently available

0:00 0:06:46 0:00

  • 16x9 Image

    Yusuf Harande

    Yusuf Aliyu Harande, dan jaridar sashen Hausa na gidan radiyon Muryar Amurka (VOA). Dan asalin Hiliya a karamar hukumar Tambuwal, jihar Sakkwato.

Facebook Forum

XS
SM
MD
LG