Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Mahaifiyar Jaruma Nafisa Abdullahi Ta Rasu


Jarumar Kannywood Nafisa Abdullahi
Jarumar Kannywood Nafisa Abdullahi

Mahaifiyar Nafisa Abdullahi, daya daga cikin fitattun jaruman Kannywood ta rasu.

A yau Talata, jaruma Nafisa ta sanar da rasuwar mahaifiyarta a shafinta na Instagram, inda ta sanya bakin shafi domin nuna yanayi na alhini da take ciki.

“Inna lillahi wa’inna ilaihi, mun rasa komai a yau” Nafisa ta rubuta da harshen larabci da Ingilishi a shafinta na Instagram mai taken nafeesat_official.

Ta kara da cewa, “shi ke raya wa, shi ke kashewa, kuma babu wanda ya isa ya hana shi yadda ya so.”

Tuni jarumai irinsu Ali Nuhu, Maryam Booth, Rahama Sadau da dumbin masoyanta suka yi ta mika sakon ta’aziyyarsu ga jarumar.

“Allah ya jikan Mama.” Inji Ali Nuhu

“Allah ya jikan Mama, Ubangiji Allah ya saka mata da Aljannatul Firdaus!!, Ameen thumma Ameen.” Inji Rahama Sadau a shafinta na instagram mai taken rahamasadau.

  • 16x9 Image

    Mahmud Lalo

    Dan jarida ne da ke aiki a Sashen Hausa na Muryar Amurka (VOA) a birnin Washington, DC na Amurka. Yana da kwarewa a rassa daban-daban na kafafen yada labarai, kamar wajen hada rahoto a takadar/mujallar jarida, fannin talbijin, rediyo, yanar gizo da kafafen sada zumunta na zamani, inda ya fi mayar da hankali kan batutuwan da suka shafi shugabanci na gari, ayyukan dogaro da kai, kiwon lafiya da kuma muhalli.

Facebook Forum

XS
SM
MD
LG