Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Rahma Sadau Ta Sami Lambar Yabo A New York


Rahama Sadau

Fitacciyar Jarumar fina finan Kannywood da Nollywood Rahma Sadau ta sami lambar yabo a Birnin New York, a yayin da ake gudanar da bikin baje kolin fina finai na ‘Women Illuminated Film Festival’ wanda kungiyar Mata ta Majalisar Dinkin Duniya ta shirya a ranar 12 ga watan Maris.

Bikin baje kolin fina finan na mata anyi shine tsawon awoyi 12, wannan biki dai anyi shine don haska mata masu shirin fina finai a fadin duniya da aka yi su kan karawa mata kwarin gwiwa, Fataucin mata, Auren wuri ga yara kanana, Ilimi da kuma Tabbatar da shari’a kan aldalci.

Rahma ta saka hoton ta rike da kambun da ta karba a yayin wannan taro a shafinta na Instagram.

  • 16x9 Image

    Ibrahim Jarmai

    Ibrahim Jarmai, ma’aikacin jarida (International Broadcaster Multi Media) a sashen Hausa na muryar Amurka, mai gabatar da shirye shirye a radio da talabijin, da kuma shafukan yanar gizo, dan asalin jihar Kasina.

Facebook Forum

XS
SM
MD
LG