Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Za'a Kera Mota Kudirin "Mission E" Mai Tafiya A Sararrin Samaniya


Shahararren kamfanin kera motocin alfarma na Porsche, ya ayyana niyar sa ta kera motocin haya masu tashi sama, kamfanin ya bayyana cewar yana cigaba da gudanar da bincike, don ganin an samar da motar nan da shekaru kadan masu zuwa.

Kamfanin ya dauki alwashin kawo karshen matsalar cinkoso a manyan garuruwa, musamman wanda kai kawon motoci ke haddasawa, a cewar mai magana da manema labarai na kamfanin Mr. Michael Steiner, wanda ya bayyana hakan a birnin Geneva, lokacin taron gabatar da motocin na kasa-da-kasa a karo na 88 a kasar Switzerland.

Kamfanin tare da hadin gwiwar kamfanin dake yunkurin kera motar tsere da aka yi ma lakabi da 911, zasu hada hannu wajen ganin sun kirkiri mota mai tafiya a cikin sararrin samaniya, ganin yadda sauran kamfanoni a duniya ke kokarin kera motoci masu tuka kansu.

Su kuwa nasu cigaban na kimiyya da fasaha, ya wuce kera mota mai tuka kanta, nasu na kera mota da zata biya bukatar jama’a cikin sauki da yanayi na gaggawa ne.

Sai ya kara da cewar “yunkurin mu shine mu kawo ma jama'a saukin gudanar da mu’amalar su ta rayuwar yau da kullun, musamman idan aka yi la’akari da yadda ake samun gosulo a cikin manyan birane, burin su shine kowa yayi tukin mota cikin walwala batare da matsalar cinkoso ba”

  • 16x9 Image

    Yusuf Harande

    Yusuf Aliyu Harande, dan jaridar sashen Hausa na gidan radiyon Muryar Amurka (VOA). Dan asalin Hiliya a karamar hukumar Tambuwal, jihar Sakkwato.

Facebook Forum

XS
SM
MD
LG